Gwamnatin Tarayya ta ƙara ayyana ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu, a matsayin ranar hutun Sallah a kasar nan.
Wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar, ta kuma yi wa al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.
Hutun dai an yi niyar yin shi a ranar Laraba, sai dai kin ganin watn Ramadana ne ya sanya aka kara mayar da hutun zuwa ranar Alhamis.