Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin 17 da Talata 18 ga watan Yunin nan a matsayin ranakun hutu, domin bukukuwan babba Sallah.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Abuja.
Tunji-Ojo ya bukaci al’umma da su ci gaba da koyi da tare da samar da zaman lafiya da kuma amfani da wannan lokacin wajen yi wa kasa addu’o’in hadin kai da wadata.
Ministan ya bada tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya baki daya.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya taya al’ummar musulmi na gida da na waje murnar wannan rana.