Gwamnatin tarayya na bin Ma’aikatu 10, da wasu hukumomi bashin Naira Tiriliyan 5.2, Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare ta Kasa, Zainab Ahmed ta bayyana hakan.
Da take bayyana hakan jiya a wajen kaddamar da wani shiri na tantance basussuka da bayar da rahoto a jiya, a Abuja, ministan ta yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta kwato naira biliyan 53.5 daga sama da hukumomin basussuka 5,000 da aka bazu a sama da MDA 10 a cikin 12 zuwa 18 da suka wuce.
Ta ce, “Bayan fitowar daftarin kudi, ma’aikatar, ta hanyar karfafa aikin, ta samu damar tara manyan basussuka na kusan naira tiriliyan 5.2. Waɗannan basussukan sun fito fili daga bayanan da aka tattara daga masu bi bashi sama da 5,000 a cikin MDAs 10. Aiki tare da ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), mun samu nasarar kwato zunzurutun kudi har Naira biliyan 53.5 a cikin watanni 12 zuwa 18 da suka wuce, ta hannun Hukumar Integrated Financial Management Information System (GIFMIS)“.
Ta kara da cewa, domin karfafa kokarin aikin, an tsara takardar neman karbo basussuka, wanda sabon sashin dawo da basussuka zai sa ido.
Zainab Ahmed ta lura cewa, duk da yadda ake amfani da fasahar kere-kere a duniya mai cike da bayanai, gwamnati ba ta da al’adar yin amfani da bayanai don jagorantar tsarawa, aiwatarwa da tantance tasirin tsare-tsare da manufofinta ko ma wajen aiwatar da muhimman ayyuka.