fidelitybank

Gwamnati ta bani lauyan kariya – Wanda ake zargi da kisan Hanifa

Date:

Wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar mai shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, ya faɗa wa kotu cewa ba shi da lauya sannan ya buƙaci gwamnatin jihar ta sama masa lauyan.

“Ba mu da lauya a yanzu saboda ba ma iya magana da kowa, amma ina roƙon gwamnati ta ba mu lauya,” in ji Abdulmalik a zaman kotun na yau Litinin.

Su ma sauran mutum biyun; Fatima da Hashin Isiyaku, sun amince da abin da Abdulmalik ya faɗa na neman lauyan.

Lauyan gwamnati Musa Lawal ya ce, gwamnatin za ta ba su lauyan kamar yadda suka buƙata. Da ma dai haka doka ta tanada saboda laifin da ake zargin su da aikatawa mai girma ne.

Mai Shari’a Sulaiman Na Abba ya ɗaga zaman shari’ar zuwa 14 ga watan Fabarairun 2022 da ƙarfe 2:00 na rana.  A cewar BBC.

A watan da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama mutum uku da ake zargi da sacewa da kuma kashe ‘yar shekara biyar ɗin a unguwar Dakata Kawaji da ke birnin Kano.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp