Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin 2 ga watan Mayu da Talata 3 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranakun hutu ga ma’aikata somin gudanar da bukukuwan Sallah na bana.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore.
A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya taya ma’aikatan Najeriya murnar zagayowar ranar ‘ma’aikata’ tare da karfafa musu gwiwa da su kara himma.
“Aiki shine ainihin ɗan adam. Muna raye saboda muna aiki kuma matattu ne kawai ba su da ikon yin aiki,” in ji Ministan.
Ya kuma taya al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, ya kuma bukace su da su kasance masu koyi da aiki da ruhin soyayya, zaman lafiya, hakuri, kin kai, kyautatawa da sadaukarwa.