Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu ga ma’aikata don murnar bikin Ranar Dimokuraɗiyya.
Wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta taya ‘yan Najeriya murna, tana mai cewa “dimokuraɗiyyar Najeriya ta gamu da cikas da kuma nasara kamar a ko’ina”.
A shekarar 2018 ne tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar bikin dimokuraɗiyyar zuwa 12 ga Yuni a madadin 29 ga watan Mayu da aka saba yin bikin, wadda ta yi daidai da ranar da ake rantsar da sabon shugaban ƙasa da kuma gwamnonin ƙasar.
Buhari ya sauya ranar ce da zimmar tunawa da ɗan siyasa Moshood Abiola, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yunin 1993 amma kuma gwamnatin soja ta soke sakamakonsa.