fidelitybank

Gwamnati ta amince da naira tiriliyan 1.9 don aikin gyara hanyoyi 44

Date:

Majalisar zartaswa ta tarayya a ranar Laraba, ta amince da shawarar da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta bayar na ganin kamfanin mai na ƙasa NNPC ya zuba kuɗi naira tiriliyan 1.9 don aikin sake gyara hanyoyi 44 a faɗin kasa.

Mataimaki na musamman kan harkokin ƴaɗa labaru a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Laolu Akande, shi ya sanar da haka bayan taron da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Akande ya ce kudaden da ake sa ran kashewa sun kasance don ci gaba da aiwatar da tsarin bunkasa ababen more rayuwa ne na tituna da kuma gyara tsarin ba da harajin zuba jari na gwamnatin tarayya, kashi na biyu na NNPC Ltd da sauran rassansa.

Ya ce majalisar ta kuma amince da masu ba da kwangilar gina tituna guda tara a ƙarkashin tsarin gwaji na shirin bunƙasa manyan tituna da gudanar da ayyukansu bayan bayar da cikakken takardar shaidar bin ka’idojin kasuwanci da hukumar kula da hanyoyin samar da ababen more rayuwa ta yi na tsawon shekaru 25.

Aikin hanyoyi da aka amince a matakin farko sun hada da hanyar Benin-Asaba da Abuja-Lokoja-Onitsha-Owerri-Aba-Shagamu-a Benin da Abuja-Keffi-Akwanga-Lafia da Makurdi da hanyar Kano-Maiduguri da hanyar Enugu-Port Harcourt da Legas-Ota-Abeokuta da kuma Legas-Badagry zuwa Seme.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp