Gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan 8.3, domin siyan motoci da kayan aiki ga rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya Mohammed Dingyadi ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja.
“A yau, Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da Asusun ‘Yan Sandan Nijeriya (NPTF) don bayar da kwangilar samar da motocin aiki guda 82, kirar Toyota, domin gudanar da aikin ‘yan sandan Nijeriya yadda ya kamata a kan kudi Naira biliyan 2.2.” in ji Dingyadi.