fidelitybank

Gwamnati na za ta ci gaba da yin adalci ga duk wani addini a jihar Oyo – Makinde

Date:

Gwamna Seyi Makinde, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin adalci ga duk wani addini a jihar Oyo.

Makinde ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Ibadan, yayin wani gagarumin gangami da kungiyar matasan Musulmi ta kasa (NACOMYO), reshen Oyo, ta shirya, domin murnar shiga sabuwar shekara ta Musulunci, 1444H.

An gudanar da taron ne a filin wasa na Obafemi Awolowo dake Ibadan. A cewar People Gazette.

Gwamnan wanda mataimakin gwamna Adebayo Lawal ya wakilta, ya ce, gwamnatinsa ta kasance ta na kiyaye daidaiton addini.

A cewarsa, Musulmai 9 na daga cikin mambobi 17 a majalisar zartarwa ta jihar, yayin da sauran takwas kuma Kiristoci ne.

Ya kuma yi kira ga malaman addinin Musulunci da su ci gaba da yi wa gwamnatinsa addu’a domin samun nasara.

Gwamnan, a wajen taron, ya bayyana bayar da gudunmawar Naira miliyan 2.5 domin tallafa wa NACOMYO.

Ko’odinetan NACOMYO a jihar, Dawood Afolabi, ya yabawa gwamnatin Mista Makinde bisa ayyana ranar hutu domin murnar zagayowar ranar farko ta sabuwar shekarar Musulunci.

Afolabi ya ce, gwamnan ya dade yana magance koke-koken al’ummar Musulmi game da nade-naden mukamai da aka yi a gwamnatinsa.

Ya kuma ba wa Makinde tabbacin goyon bayan musulmin jihar “muddin kun tabbatar da adalci na addini a kowane fanni na mulki.”

Lakca mai taken ‘Zaben 2023: Musulmai da kuma tasirin rinjaye na adalci’, ya kasance wanda Afeez Oladosu ya gabatar yayin taron.

Oladosu ya bukaci Musulmin Oyo da su yi rajista tare da karbar katin zabe na dindindin (PVC) gabanin babban zabe na 2023.

Ya kuma bukaci masu zabe da su zabi shugabanni masu tsoron Allah cikin hikima a lokacin zaben.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp