Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa ta fara aikin gine-gine tare da gyara ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar ‘yan Najeriya.
Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan albarkatun ruwa Alhaji Suleiman Adamu ya bayyana haka a Birniwa yayin kaddamar da aikin titin Hadejia zuwa Nguru mai tsawon kilomita 33 wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 7.9.
Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gina tare da gyara hanyoyi da dama da kuma gadoji a fadin kasar nan daga shekarar 2015 zuwa yau.
Ya kuma gargadi hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su aiwatar da dokar takaita gudun kilomita 100 akan hanyoyin Najeriya domin rage hadurran da ba dole ba.
Har ila yau, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fasola, ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta samar da ababen more rayuwa a dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida.
Fasola ya ce an kammala ayyuka da dama kuma an kaddamar da su, yayin da wasu kuma ana kan kammala kuma nan ba da dadewa ba za a kaddamar da su.
Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yabawa gwamnatin tarayya, karkashin shugaba Buhari kan ayyukan tituna.
Gwamnan wanda mataimakinsa Malam Umar Namadi ya wakilta, ya ce jihar ta ci gajiya sosai daga ayyukan gwamnatin tarayya daga shekarar 2015 zuwa yau.