Mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya yi kira da a ƙara kaimi da kuma samar da hanyoyi na kawo karshen ababen fashewa da ƙungiyoyin ƴan ta’dda a yammacin Afrika ke amfani da wasu wajen kai hare-hare.
Ribadu ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki na ganin an haɗa kai wajen daƙile amfani da ababen fashewa a yammacin Afirka da aka buɗe a Abuja, ranar Talata.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkar tsaro ya ce barazanar ayyukan ƴan ta’dda ba su da iyaka, inda ya ƙara da cewa sai masu ruwa da tsaki sun haɗa kai, kafin za a samu damar magance matsalar.
Ya ƙarfafa gwiwar mahalarta taron cewa su shiga a dama da su ta hanyar tattaunawa, samar da hanyoyi da kuma aiki tare don laluɓo mafita da za ta taimaka wajen daƙile ayyukan ta’ddanci da ke yi wa al’ummomi a yammacin Afirka barazana.
“Muna shirin samar da dabaru na zamani waɗanda za su taimaka mana wajen daƙile amfani da ababen fashewa.
“Shawarwari da za a samu a wannan taro suna da muhimmanci wajen tsara yadda za mu kare al’ummomin mu daga barazanar ababen fashewa,” in ji Ribadu.
Shi ma lokacin da yake magana a wajen taron – jakadan Aljeriya a Najeriya, Hocine Mezoued, ya ce dole ne ƙasashen Afirka su ɗauki matakan yaƙi da ta’addanci idan har ana so kawo karshen matsalar.
Ya ce matakan za su kuma taimaka wajen daƙile sabbin hanyoyin zamani da ƴan ta’ddan ke amfani da su wajen kai hare-hare.
A cewarsa, ababen fashewa ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyi da ƴan ta’dda suka fi amfani da su wajen far wa al’ummomi a faɗin yammacin Afirka da kuma ƙasashen da ke yankin Sahel.