Gwamnatin Tarayya na can ta na wata gana wa da shugabannin ƙungiyar ƙwadago a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a ƙoƙarinta na shawo kan barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar ta yi.
Ganawar wanda shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ke jagoranta, ta na kuma ɗauke da wasu ministoci.
A makon da ya gabata NLC da takwararta ta TUC suka yanke shawarar cewa za su tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 3 ga watan Oktoba.
Ƙungiyoyin sun kuma buƙaci rassansu na jihohi da su fara shiri domin soma zanga-zanga ta ƙasa baki-ɗaya.