fidelitybank

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Date:

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kakkausar murya, yana mai cewa cikin shekara biyu kacal, gwamnatin ta nuna gazawa, kuma gwamnati ce wadda ba ta tare da jama’a sannan maras jin tausayin talakawa fiye da kowacce gwamnati tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ba za ta yi shiru ba yayin da halin rayuwa ke ƙara tsananta ga ‘yan kasa tare da yawaitar almubazzaranci daga bangaren gwamnati.

Atiku ya ce babu wata gwamnati da ta taɓa jefa al’umma cikin irin wannan ƙunci ba tare da la’akari da gaskiya da rikon amana da jagoranci nagari ba.

“Wannan gwamnati ta Tinubu ba wai kawai ta ƙara talauci a fadin ƙasar ba ne, har ma ta kafa sabbin tarihi wajen almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a.”

Ya ƙara da cewa a daidai lokacin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, jami’an gwamnati suna rayuwa cikin walwala da amincewa da kasafin kuɗi da ke amfana kawai ga attajirai yayin da talakawa ke ci gaba da shan wahala.

“Abin taƙaici ne yadda Najeriya ba wai kawai ta kasance ƙasa da ke fama da matsanacin talauci a duniya ba, yanzu haka ta zama ƙasar da ke da yawan yara masu fama da rashin abinci fiye da kowacce ƙasa a Afirka, hatta fiye da Sudan — ƙasar da ke fama da yaƙi.” in ji Atiku.

Ya ce bisa rahoton Global Hunger Index na 2024, Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da yunwa da rashin abinci, inda take matsayi na 18 a duniya.

Ya ƙara da cewa duk wani tsarin gwamnati da aka ɗauka a ƙarƙashin wannan mulki ya fi cutar da talakawa fiye da komai, yayin da masu kuɗi ke ci gaba da morewa.

Atiku ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yawan bashin da gwamnatin ke ci gaba da karɓa.

“A lokacin da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, jimillar bashin ƙasar ya tsaya kan naira tiriliyan 49. Amma cikin shekaru biyu kacal da fara mulki, ya karu zuwa tiriliyan 144 yayin da kuma ake shirin karɓar ƙarin bashi daga ƙasashen waje wanda zai iya kai bashin ƙasar zuwa tiriliyan 183.”

Atiku ya ce su a matsayin su na jam’iyyar adawa da masu kishin kasa, ba za su zuba ido ba su kalli abubuwan da ke faruwa ba su ci gaba.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp