Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya dage cewa gwamnatin tarayya ba ta tattaunawa da ‘yan ta’adda a jihar Zamfara, a yunkurin da ake na ganin an sako daliban jami’ar tarayya da ke Gusau da aka sace.
Badaru ya bayyana zargin da gwamnan jihar Zamfra, Dauda Lawal ya yi a matsayin yaudara.
A wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Hope Attari, Badaru, ya ce shugaba Bola Tinubu ya baiwa sojoji da sauran jami’an tsaro umarnin gudanar da tattaki domin ganin an sako wadanda aka sace.
“Gwamnatin Tarayya tana aiki ba dare ba rana don ganin ‘yan matan da sauran su sun koma gida,” in ji shi.
Badaru ya tabbatar wa al’ummar Zamfara da ‘yan Najeriya irin ci gaban da ake samu na dawowar dalibai mata da sauran jami’ar tarayya ta Gusau cikin gaggawa.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa rundunar hadin guiwar jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana domin ceto daliban.
Ministan ya bayyana cewa umurnin shugaban kasar ya fara samun sakamako yayin da 13 daga cikin daliban da aka sace da kuma wasu uku suka samu ‘yancinsu a ranar Litinin.
“An samu wannan nasarar ne ta hanyar kwararrun kokarin sojoji,” in ji shi.


