Mambobin kwamitin uku da suka hada da gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago sun koma tattaunawa kan sabon mafi karancin albashin ma’aikatan Najeriya.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo, ya ce gwamnatin tarayya ba ta gabatar da sabon tayin mafi karancin albashi ba a tattaunawar.
“Ba a gabatar da komai ba tukuna. Ministan kudin kasar ya ce har yanzu suna nan suna aiki kan tsarin da shugaban kasa ya umarce su da su yi aiki da shi,” inji shi.
A cewarsa, duk abin da suke tattaunawa shi ne ka’idojin da ke tattare da wasu daga cikin wadannan batutuwa, amma ba su gabatar da wani abu da ya wuce abin da aka gabatar a baya ba.
Don haka ya bayyana fatansa na cewa idan suka sake zama za su sami abin da za su ji.
Wale Edun, ministan kudi ne ya wakilci gwamnatin tarayya a taron; Atiku Bagudu, ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa; da Nkeiruka Onyejeocha, ministan kwadago.
Wakilan sakataren gwamnatin tarayya da kuma shugaban ma’aikata na tarayya sun halarci taron.
Ga kungiyar kwadago, Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), da Osifo sun halarci taron.
Abdulateef Shittu, darakta-janar na kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), shi ma ya halarta.
Ku tuna cewa kungiyar kwadagon a ranar Litinin din da ta gabata ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunsu na sabon mafi karancin albashi.
Kungiyar kwadagon ta gabatar da kudirin N615,500 da N494,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa, wanda gwamnati ta ce ba gaskiya ba ne.
A ranar Talata, kungiyar kwadagon ta sassauta aikin masana’antu na tsawon mako guda don ba da damar tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi.