Gwamnan jihar Ribas kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Nyesom Wike, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na ranar Asabar, ya zargi gwamnonin Kudu da cin amanar yarjejeniyar sauya madafun iko.
Wike, wanda ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar tare da marawa dan takararta na shugaban kasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa, ya kusa yin kaca-kaca da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a wani mataki da aka saba wa doka amma sai da ya nutsu.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wani liyafar karrama shi da aka yi a gidan gwamnati da ke Fatakwal, Jihar Ribas, bayan dawowar sa daga zaben fidda gwani na shugaban kasa a Abuja.
Har ila yau, ana ci gaba da yabo ga Atiku kan fitowar sa a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP, a jiya, kamar yadda kungiyar al’adun kabilar Igbo ta Igbo, Ohanaeze ta musanta cewa, za ta yi aiki da Atiku, inda ta kara da cewa ba ta da wani matsayi a kan batutuwan.