fidelitybank

Gwamnan Zamfara ya mayarwa ƙasurgumin ƴan ta’adda sarautar sa

Date:

Gwamnan jihar, Muhammed Bello Matawalle, ya mayar wa Aliyu Garba Marafa sarautarsa ta sarkin Birnin Yandoto.

A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnan ya dakatar da sarkin saboda ya bai wa jagoran ‘yan bindiga Ado Aleiru sarautar sarkin Fulani a fadarsa.

Naɗin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar.

A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe Sardauna ya fitar ne ta tabbatar da mayar da sarkin kan karagarsa.

Sanarwar ta ce an mayar da sarkin ne sakamakon buƙatar hakan daga kwamitin da gwamnati ta kafa domin bincike kan lamarin.

Tun da farko dai sarki ya ce ya bai wa Ado Aleiru sarautar ne sakamakon rawar da ya taka wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin masarautar da ‘yan bindigar da ke addabar ƙaramar hukumar Tsafe. In ji BBC.

Sanarwar ta kara da cewa ”kwamitin bai samu wata hujja da ke nuna cewa sarkin na da wata mummunar manufa game da naɗin Ado Aleiru, ko haɗin baki tsakanin sarkin da ‘yan bindiga”.

“Sakamakon binciken kwamitin ya nuna cewa an naɗa Ado Aleiru ne a wani ɓangare na samar da zaman lafiya tsakanin tubabbun ‘yan bindiga da kuma garuruwan da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Tsafe da Gusau, wanda ya haɗa da garin Yandoto, don haka gwamnati ta mayar da sarkin ba tare da ɓata lokaci ba”.

thisday nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp