Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya kori Hon. Kabiru Sahabi Liman a matsayin mai ba shi shawara na musamman.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balalabe ya sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.
Ya ce Gwamnan ya ga ya zama dole a soke nadin.
A cewar sanarwar, hakan ya biyo bayan wani atisayen sa-ido da aka yi, wanda ya nuna, da dai sauran abubuwa, da cewa bai da karfin gudanar da ayyuka da kuma kishin jama’a da ke da alaka da daukakar matsayin mai ba da shawara ta musamman.
Ya ce aikin sa ido zai kasance mai ci gaba da gudana, da nufin inganta ayyukan yi wa jama’a, tabbatar da amincewar jama’a da kuma samar da kyakkyawan shugabanci a jihar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana laifin da mai ba shi shawara na musamman ya aikata ba.


