Gwamnan jihar Zamafar Dauda Lawal Dare ya bai wa al’ummar yankin Gummi da suka fuskanci bala’in ambaliya tallafin naira miliyan 100.
Cikin wata sanarwa da sakatare yaɗa labaran gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnan ziyarci garin Gummi ranar Asabar, domin jajanta wa mutanen da bala’in ambaliyar ta shafa.
Garin Gummi ya fuskanci mummunar ambaliya a ‘yan kwanakin baya-bayan nan , lamarin da ya haddasa asarar dukiya mai dimbin yawa.
Dauda Lawal ya ce ya je garin ne domin jajanta wa mutanen garin kan abin da ya faru.
Gwamnan ya kuma kai musu kayayyakin tallafi domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi a lokacin ambaliyar.
“Ina so na yi amfani da wannan damar don sanar da ku cewa na ba ku tallafin buhu 10,000 na abinci da ya haɗa da shinkafa da masara da gero domin raba wa mutane da bala’in ya shafa. Haka kuma a madadin gwamnatin jihar Zamfara na bayar da tallafin naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ta shafa”, in ji shi.
Gwamnan ya kuma ƙara da cewa gwamnati za ta bai wa mutanen da ambaliyar ta shafa filaye a wuraren da ba su da hatsarin ambaliya domin sake gina gidajensu.