fidelitybank

Gwamnan Zamfara ya baiwa Ɗalibai aiki su 16 da yaƙin Sudan ya koro su

Date:

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bai wa ɗaliban jihar su 16 da suka karanci aikin jinya, a jami’ar Sudan aiki.

A ranar Alhamis ne gwamnan ya gabatar wa ɗaliban takardunsu na shaidar kammala karatu da jami’ar ta aiko musu a fadarsa gwamnati da ke birnin Gusau.

Cikin wata sanarwar da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ya ce a 2023 ne gwamnatin jihar ta kwaso ɗaliban Zamfara 66 da ta tura Sudan domin karatu bayan ɓarkewar rikicin ƙasar.

”16 daga cikin ɗaliban masu karantar aikin jinya ne da ke shekarar ƙarshe a karatunsu, waɗanda jarrabawar ƙarshe ce kawai ta rage su kammala karatun, inda gwamnatin jihar ta ɗauki matakin taimaka wa ɗaliban”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta haɗa kai da hukumar gudunarwar jami’ar, domin bai wa ɗaliban 16 damar rubuta jarrabawar tasu ta ƙarshe, wadda aka yi a Najeriya.

Daga nan kuma jami’ar ta aika wa ɗaliban takardun shaidar kammala karatun nasu, wadda kuma gwamnan ya gabatar musu a lokacin da ya yi musu albishirn ba su aikin a gwamnatin jihar.

Warning
Warning
Warning
Warning

Warning.

vanguardnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hogan ya mutu bisa cutar gazawar koda

An bayyana cikakkun bayanai game da mutuwar ɗan wasan...

Sojoji sun kashe rikaken dan Bindiga Dan Dari Biyar a Sokoto

Dakarun Operation FANSAR YANMA sun yi nasarar fatattakar wani...

An kashe utane 30 a yakin Thailand da Cambodia

An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka...

Ba mu ƙayyade shekarun shiga ƙaramar sakandare JSS1 – Ma’aikatar Ilimi

Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu...

Ido da Ido na ga yadda Sojojin Isra’ila ke kashe Falasdinawa – Tsohon Sojin Amurka

Wani tsohon sojan Amurk ya ce, ya ga yadda...

‘Yan majalisar Birtaniya 220 na neman ƙasar ta amice da ƙasar Falasɗinu

'Yan majalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta...

Buhari yaki karbar kyautar Agogon lu’u-lu’u da jirgin sama – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

An kama wanda ya kashe tsohuwar Matarsa a Jigawa

Ƴansandan Jihar Jigawa sun ce, sun kama wani mutum...

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan Kwankwaso

Fadar shugaban kasa, ta mayar wa tsohon gwamnan Kano...

Barau FC ta naɗa Ladan Bosso sabon kocinta

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da...

Am fara dawo da ‘yan Najeriya daga Afrika ta Tsakiya

Hukumomi a Najeriya sun ce, sun fara ƙoƙarin mayar...

G-Fresh da Hamisu Breaker sun samu gurbi kurkuku bayan sun watsa Naira

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ɗaure shahararrun...
X whatsapp