Gwamnan jihar Taraba mai barin gado, Darius Ishaku, ya sha kaye a takarar kujerar Sanatan Taraba ta Kudu.
Ɗan takarar jam’iyyar APC David Jimkuta ne ya yi nasara bayan samun kuri’u 85,415.
Darius Ishaku shi ne ya zo na biyu a zaɓen da kuri’u 45,708.
Haka nan ma, Sanata Shu’aibu Isa Lau na jam’iyyar PDP, shi ya sake samun nasara a kujerar Sanatan Taraba ta Arewa da kuri’u 74,645, inda ya doke abokin adawarsa na APC Sani Abubakar Danadi wanda ya samu kuri’u 61,878.
A takarar Sanatan Taraba ta Tsakiya kuma, Haruna Manu shi ya lashe zaɓe da kuri’u 76,460, inda ya kayar da Bashir Marafa Abba na APC wanda ya samu kuri’u 52, 437.