fidelitybank

Gwamnan Sokoto ya tsige Hakimai 15 a kan karagar mulki

Date:

Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya tsige Hakimai 15 daga kan karagar mulki, bisa zarginsu da laifin rashin biyayya, satar filaye, taimakon rashin tsaro da kuma karkatar da kadarorin gwamnati.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamna Abubakar Bawa ya fitar ranar Talata a Sokoto.

Daga cikin Hakiman da aka tsige akwai: Unguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, lllela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da gundumar Giyawa.

Sauran su ne wadanda tsohon Gwamna Aminu Tambuwal ya nada a karshen gwamnatin sa.

“An soke su ne saboda yanayin nadin da aka yi musu wanda a cewar sanarwar an yi su ne cikin gaugawa da kuma kin amincewa da mutanensu.

“They are Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun Yar Tsakkuwa, Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Torankavwa,” in ji sanarwar.

A cewar sanarwar, an ba da shawarar kararrakin da suka shafi Hakiman Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi don ci gaba da bincike.

Hakazalika Sarkin Yakin Binji, babban mai ba da shawara a Majalisar Sarkin Musulmi, an mayar da shi Bunkari yayin da Hakimin Sabon Birni ya kai Gatawa.

Bawa ya kuma lura cewa wasu Hakimai bakwai gwamnati ta rike.

Sun hada da Alhaji Aliyu Abubakar III Churoman Sokoto, Alhaji Ibrahim Dasuki Maccido Barayar Zaki, Abubakar Salame Sarkin Arewan Salame, da Aminu Bello Sarkin Yamman Balle.

Others are Mahmoud Yabo Sarkin Gabas Dandin Mahe, Mukhtari Tukur Ambarura Sarkin Gabas Ambarura da Malam Isa Rarah Sarkin Gabas na gundumar Rarah.

Hakiman Tsaki da Asare su ma an ci gaba da rike su, yayin da Abdulkadir Mujeli wanda aka nada a matsayin Magajin Garin Sokoto aka bukaci ya koma kan mukaminsa na tsohon Sarkin Rafin Gumbi.

Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan shawarwarin kwamitin duba nade-nade na Sarakunan gargajiya, da sauya sunayen manyan makarantu da kuma rusa majalisun kananan hukumomin jihar da gwamnatin jihar ta kafa.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp