Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya bai wa al’ummar yankin Sabon Birni da ayyukan ƴan bindiga ya shafa tallafin sama da naira miliyan 20 tare da rarraba magunguna da kayan abinci.
Ya kuma yi alƙawarin ɗaukar nauyin kuɗin maganin mutanen da suka ji rauni sakamakon hare-haren ƴan bindiga a ƙaramar hukumar da ke jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ziyarar da ya kai tare da Sanata Aliyu Wamakko zuwa ƙaramar hukumar domin jajanta wa mutanen da hare-haren ƴan bindiga suka shafa.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Gwamnan ya ce zai ci gaba da tallafa wa al’ummar yankin tare da kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a jihar.
Ya kuma bayyana damuwa kan faruwar hare-haren inda ya ce yana matuƙar kaɗuwa duk lokacin da aka samu afkuwar harin ƴan bindiga a wani yanki na jihar.
A cewarsa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba domin daƙile matsalar rashin tsaro a jihar ta Sokoto.
Ahmad Aliyu ya kuma ce za su ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro inda ya sanar da basu motoci 100 da kuma horas da ƴan vigilante 2,000 domin su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Ya ƙara da cewa za a bai wa ƴan vigilanten babura 700 domin sauƙaƙa ayyukansu ƙarƙashin kulawar hukumomin tsaro.


