Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya kada kuri’arsa.
Makinde ya kada kuri’a ne a unguwar Abayomi, dake kan titin Iwo, a Unit 001, Ward 11 a karamar hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas a Ibadan.
Ya isa rumfar zaben da misalin karfe 10:32 na safe.
Karanta Wannan: An samu fitowar jama’a a jihar Jigawa
Gwamnan wanda ke neman wani wa’adin mulki a karkashin jam’iyyar PDP, ya je kada kuri’arsa nan take ya isa wurin taron.
Jama’a da dama ne suka yi masa maraba da kuma jiran isowarsa.
Daruruwan jama’a sun sa gwamnan ya kasa yin magana da ‘yan jarida.