Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a zaben 2023 a karo na biyu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis.
An zabi Makinde a matsayin gwamna a shekara ta 2019 a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya kayar da dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a lokacin, Adebayo Adelabu da ‘yan takarar wasu jam’iyyun siyasa, domin ya zama gwamna a 2019.
Makinde, a yayin da yake bayyana muradinsa na sake tsayawa takara a karo na biyu, ya ce, ya sayi fom din nuna sha’awa da tsayawa takara a jam’iyyar PDP.
Ya ce, zai sake yin shekaru hudu a kan karagar mulki idan al’ummar Jihar suka so.