Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Talata ya bi sahun kungiyoyin kwadago da sauran kungiyoyinsu a wata zanga-zangar lumana.
Da yake shiga zanga-zangar, Makinde ya tabbatar wa jama’a cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen radadin da ake ciki a kasar nan.
Masu zanga-zangar da yawansu ya kai dari ne suka tarbi gwamnan da ihu yayin da shugaban kungiyar ta Oyo, Kayode Martins ke jawabi ga masu zanga-zangar.
Makinde ya ce yana sane da halin kuncin da jama’a ke ciki, inda ya yi alkawarin cewa zai kasance cikin al’ummar da za su gyara kasar nan.
Ya ce ya mayar da martani ga shugaban NLC na kasa, Joe Ajero wanda ya yi ikirarin cewa babu wata jiha a kasar nan da ke biyan albashin ma’aikata.
Ya kuma tabbatar wa da ma’aikatan cewa za a kai wasikun zanga-zangar da korafe-korafen su ga shugaban kasa Bola Tinubu.