fidelitybank

Gwamnan Oyo ya bayar da umarni a binciki wata Islamiyya da ta yi taro Yara da dama suka mutu

Date:

 

Rahotanni na cewa wani mummunan turmutsutsu da aka samu a wata makarantar Islamiyya a birnin Badun (Ibadan) na jihar Oyo, ya janyo mutuwar kananan yara da dama jiya Laraba.

Lamarin ya faru ne a unguwar Bashorun, yayin wani biki da yaran ke gudanarwa, sai dai har kawo yanzu, ba a hakikance adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

Wata sanarwar kwamishinan watsa labaran jihar Dotun Oyelade, ta ce an kwashi wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka zuwa asibitoci daban daban da ke kwaryar birnin domin kula da lafiyarsu.

Zuwa yanzu ba a bayyana musabbabin faruwar lamarin ba, sai dai mazauna yankin sun ce sama da yara dubu biyar ne suka taru a wurin da ake gudanar da bikin, inda masu shirya gasar suka yi alkawarin bayar da muhimman kyautuka, ciki har da tallafin karatu.

Turmutsutsun ya soma ne lokacin da manyan masu shirya taron suka isa wurin da za a fara taron.

“Ana kira ga iyayen da ke neman inda ‘ya’yansu suke da su duba asibitocin da suke kwance domin tantance ko suna wuraren” inji kwamishinan watsa labaran jihar.

Gwamnan jihar ta Oyo, Seyi Makinde, ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter wato X, inda ya ce an dauki kwararan matakai don ganin hakan ba ta sake faruwa ba, kana za a gudanar da bincike don gano ainihin abun da ya faru.

Ya kara da cewa za a hukunta duk wanda aka gano yana da hannu a faruwar bala’in.

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp