Mai magana da yawun Sanata Ademola Adeleke, Olawale Rasheed, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Osun ba ta nuna shirin bayar da hadin kai ga kwamitin mika mulki da zababben gwamnan ya kafa.
Hakan na zuwa ne kamar yadda kwamitin ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Adegboyega Oyetola ba ta nuna wata alamar shirin kafa kwamitin mika mulki nata ba.
Zababben gwamnan jihar Osun, a ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli, 2022, ya kaddamar da kwamitin mika mulki na mutum 37 da aka dorawa alhakin tuntubar kwamitin da gwamnatin jihar za ta kafa domin tabbatar da mika mulki daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar PDP.
Mai magana da yawun Sanata Ademola Adeleke, Olawale Rasheed ya bayyana cewa gwamnatin jihar Osun ba ta nuna shirin bayar da hadin kai ga kwamitin mika mulki da zababben gwamnan ya kafa.
Hakan na zuwa ne kamar yadda kwamitin ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Adegboyega Oyetola ba ta nuna wata alamar shirin kafa kwamitin mika mulki nata ba.
Olawale, wanda ya bayyana cewa har yanzu jam’iyyar APC ta kasa shawo kan kaduwar kayen zaben gwamnan da aka yi a ranar 16 ga watan Yuli, ya nuna cewa gwamnatin mai barin gado ba ta da sha’awar bayar da hadin kai ga kwamitin mika mulki.
“Dukkanmu mu yi wa mutanen Osun aiki, Gwamna Oyetola, zababben gwamnan mu da mu shugabanni.
“Wannan shi ne lokacin da za mu taru don tabbatar da mika mulki ba tare da wata matsala ba. Suna ba mu bayanai kan abubuwan da ke faruwa, mu ma muna shigar da su, domin al’ummar Jihar Osun a karshen wannan rana za su ji dadin hakan.