Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu a jihar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya fitar, ya ce hutun zai bayar da dama ga ‘yan jihar su karɓi katin zaɓensu a wurare daban-daban da hukumar zaɓen ta ware domin karɓar katin a faɗin jihar.
”Babban zaɓen da ke tafe na da matuƙar muhimmanci, dan haka ya kamata mu magance matsalar ƙarancin karɓar katin zaɓe da shiyyar kudu maso yamma ke fuskanta”, in ji sanarwar.
A ranar 25 ga watan Fabrairun da ke tafe ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.