Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2023 ya zama doka.
Da yake rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudi na Naira 472,250,694,447.57b kamar yadda majalisar dokokin jihar ta amince da shi a baya, a ranar Alhamis, Abiodun ya ce, zai tabbatar da cikakken aiwatar da dukkan abubuwan da ke cikin kudirin don dorewar ci gaban ajandar Gina Makomarmu ta Gwamnatin sa.
“Wannan kasafin kudin ya na nuni ne da abin da al’ummar jihar Ogun ke bukata. Ina tabbatar muku cewa a namu bangaren, za mu tabbatar da aiwatar da kasafin kudin.
“Ta hanyar wannan kasafin kudin, jama’armu za su ci moriyar dimokuradiyya,” in ji shi.
Ya godewa shugaban majalisar da ’yan majalisar bisa jajircewarsu da suka yi har aka kammala zartar da kasafin kudin kafin karshen shekarar 2022.