Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, ya kafa dokar hana fita a garin Lambata dake karamar hukumar Gurara ta jihar, biyo bayan wani kazamin fada da yayi sanadiyar mutuwar hakimin Lambata Mohammed Abdulsafur.
Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jamiāin yada labarai na ofishin SSG, Lawal Tanko ya fitar.
Matane ya kara da cewa gwamnan ya bada umarnin a sanya dokar hana fita a garin na Lambata daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe daga ranar Lahadi 15 ga watan Janairu, 2023 har zuwa wani lokaci.
SSG ta bayyana cewa an sanya dokar ne domin a taimakawa jamiāan tsaro wajen daidaita alāamura a yankin, da ceton rayuka, da kuma ba da damar maido da doka da oda.
A cewarsa, āGwamnati ta yi Allah wadai da taāaddanci da rashin bin doka da oda da aka samu a garin Lambata.ā
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna yankin da su baiwa jamiāan tsaro hadin kai a aikin gaggawa na maido da zaman lafiya a garin Lambata, yayin da ta bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar hana fita.