Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi afuwa ga fursunoni 14 da ke zaman gidan yari daban-daban a cibiyoyin tsare tsare a jihar.
Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Mista Labaran Magaji ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a garin Lafiya.
Kwamishinan ya ce matakin da gwamnan ya dauka na amfani da ikon da aka ba shi a karkashin sashe na 212 (1) da (2) na kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara).
A cewarsa, Sule ya gudanar da aikin ne bisa ga ikon da aka ba shi da kuma tuntubar majalisar ba da shawara kan jin kai ta jiha.
Magaji ya kara da cewa gwamnan ya saki fursunonin ne domin tunawa da ranar 1 ga watan Janairun 2024.
Ya ce fursunonin da aka saki sun hada da: Sani Musa, Mohammed Maji, Danjuma Anthony, Ali Mohammed, Yahuza Turaki, Ibrahim Musa da Abdullahi Usman.
Sauran sun hada da: ThankGod Ayaba, Usman Idris, Adamu Sule, Terzungwe Mshi, Shehu Abubakar, Zacheous Ayuba da Surajo Abdullahi.
Babban Lauyan ya bukaci fursunonin da su kasance masu bin doka da oda kuma su guji aikata duk wani laifi da zai mayar da su wuraren da ake yi musu gyara.