Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda hudu a ma’aikatan jihar.
Shugabar ma’aikatan Mrs Abigail Waya ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai ranar Litinin a Lafiya, babban birnin jihar.
Sabbin sakatarorin dindindin da aka nada sun hada da John Ali Damina daga Akwanga, Florence Yakwari daga Karu, Ezekiel O. Enga daga Nasarawa Eggon da Isma’ila Ali Mohammed daga karamar hukumar Keffi.
Waya ya ce nan ba da jimawa ba za a bayyana ranar da za a rantsar da su.


