Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin dawowa a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna na 2023.
Ahmed Ibeto, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar, ya sanar da Sule a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana a garin Lafia babban birnin jihar a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu, 2022.
A cewar Ahmed, Sule ya samu kuri’u 698 inda ya doke Fatima Abdullahi wadda ta samu kuri’u uku.
“Da wannan sakamakon, dangane da abin da ya shafi mu da kuma matsayina na shugaban wannan kwamitin na fidda gwani, na bayyana Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna,” in ji shi.