Hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana gwaman jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Farfesa Tanko Ishaya ne ya bayyana haka, inda ya ce Abdullahi sule na APC ya lashe zaɓen bayan da ya samu yawaun ƙuri’u 347,209.
Abdullahi Sule ya doke babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP David Ombugadu wanda ya samu ƙuri’a 283,016.