Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Litinin ya jajanta wa jamâiyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), bisa rasuwar magoya bayanta a wani yamutsi.
Wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP sun mutu a wani hatsari a ranar Asabar bayan wani gangamin maraba da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa-Kwankwaso zuwa jihar.
Sakon na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahim Adra kuma ya mika wa manema labarai ranar Litinin a Lafiya.
Mista Adra, a cikin sanarwar, ya ce gwamnan ya nuna bakin cikinsa kan hadarin.
âGwamnan ya bayyana asarar rayukan âyan kasa a irin wannan yanayi a matsayin abin bakin ciki kuma ya bukaci jamâiyyun siyasa da magoya bayansu da su yi taka-tsan-tsan a kowane lokaci,â in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya jajantawa iyalai da abokanan wadanda suka rasu da kuma shugabannin jamâiyyar.


