Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa ma’aikatan gwamnati daga mataki na 1 har zuwa na 14 za su fara zuwa aiki kwana uku a mako a wani mataki na saukaka kalubalen tattalin arzikin da mazauna yankin ke fuskanta.
Ya yi magana ne a wata hira ta kai tsaye a kafafen yaɗa labarai, ‘Sanwo Speaks’, domin jan hankalin mazauna yankin kan matakan da ake dauka na rage nauyin raɗadin tattalin arzikin da ke kan ‘yan Legas.
Amma kuma ma’aikata a sashen koyarwa za su ci gaba da zuwa aiki na kwanaki biyar a mako wanda ya ce gwamnati za ta tabbatar a ƙara musu tallafin sufuri.