Gwamnatin jihar Katsina ta rattaba hannu da wani kamfanin kasar Faransa mai suna Ocean Solutions Energie domin bunkasa wutar lantarki a jihar.
Yarjejeniyar ta yi daidai da dokar samar da wutar lantarki ta 2023 wacce ta karkasa hanyoyin samar da makamashi da hade hanyoyin da ake sabunta su a cikin wutar lantarkin Najeriya.
Har ila yau, yana cikin cika burin ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya (SDGs) 7 akan makamashi mai araha da tsafta.
Gwamnan jihar, Malam Dikko Radda da mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin wutar lantarki da makamashi, Dakta Hafiz Ahmed, sun sanya hannu kan yarjejeniyar, bayan wata tattaunawa da takwarorinsu na ci gaba da masana’antu a birnin Paris na kasar Faransa.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Ibrahim Mohammed, a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, ya ce kamfanin na kasar Faransa wanda ya kware wajen bunkasa ayyukan makamashi a nahiyar Afirka, ya samu wakilcin shugaban kamfanin, Mista Minkaila Salami.
Sanarwar ta ce: “A bisa wadannan manufofi, Gwamna Radda ya bayyana shirin kafa wata karamar tashar samar da wutar lantarki a wani bangare na aikin gwaji.
“Gwamnan ya lura cewa shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da ingantaccen makamashi mai sabuntawa ga al’ummomin yankin kuma zai zama abin koyi ga ci gaban wutar lantarki a nan gaba a fadin madatsun ruwa 43 na jihar.
“Gwamnatin jihar Katsina ta kuduri aniyar bayar da tallafin kudi domin ganin an samu nasarar girka tashar wutar lantarki da kuma dorewar dogon lokaci.”