fidelitybank

Gwamnan Katsina shiga tawagar jami’an tsaro na yakar ‘yan bindiga

Date:

Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda, ya shiga tawagar jami’an tsaro don daƙile wani harin da ‘yan bindiga suka suka ƙauyen Zakka da ke ƙaramar hukumar Safana a jihar.

Cikin wata sanarwa da satakaren yaɗa labaran gwamnan, Kaula Mohammed, ya fitar, ya ce tawagar jami’an tsaron ta samu nasara kuɓutar da wani mutum mai shekara 33 da ‘yan bingidar suka kama a lokacin da suka kai harin.

Sanarwar ta ce, da farko gwamnan ya je Safana ne domin ƙaddamar da wani shirin tallafi da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Abduljalal Runka, ya shirya a lokacin da ak yi wa jami’an tsaro kiran gaggawa kan harin da ‘yan bindigar suka kai ƙauyen na Zakka.

Bayan samun rahoton ne kuma, sai gwamna ya gaggauta katse taron da yake halarta, inda nan take ya nufi ƙauyen tare da sauran jami’an tsaro.

“Gwamna Radda tare da wasu mambobin tawagarsa sun i sahun jami’an tsaro da suka haɗar da ‘yan sanda da sojojin saman rundunar Hadarin Daji, da na ƙasa, da kuma jami’an tsaron sa-kai da ya ƙaddamar”, in ji sanarwar

An yi arangama da ‘yan bindigar kafin su tsre zuwa cikin tsaunuka.

“Bayan fafatawa mai zafi na tsawon miti 30 da ‘yan bindigar, jami’an tsaron sun samu nasarar kuɓutar da wani mutum mai shekara 33”

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan bindigar sun tsere ba tare da kashe wasu daga cikinsu ba.

Bayan daƙile hari ne kuma, Gwamna Radda ya bayar da umarnin gaggauta kai mutumin da aka ƙubutar asibiti bayan da ‘yan bindigar suka harbe shi a ƙafa, in ji sanarwar.

Dama dai gwamnan ya sha yin alwashin shiga daji domin yaƙar ‘yan bindiga a lokutan yaƙin neman zaɓensa.

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp