fidelitybank

Gwamnan Kano ya sosa wa wasu Kwamishinoni baya da manjagara tare da yin garambawul

Date:

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da gyare-gyare a majalisar zartarwar jihar, inda ya cire wasu, sannan ya sauya wa wasu ma’aikatu.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya soke ofishin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, wanda Alhaji Shehu Wada Sagagi ke riƙewa, sannan ya sauke sakataren gwamnatin jihar, Dokta Baffa Bichi saboda rashin lafiya.

Sanarwar ta ce gwamnan ya cire kwamishinoni guda biyar: Ibrahim Jibril Fagge na ma’aikatar kuɗi da Ladidi Ibrahim Garko ta ma’aikatar al’adu da yawon buɗe ido da Baba Halilu Dantiye na ma’aikatar watsa labarai da Shehu Aliyu Yammedi na ma’aikatar ayyuka na musamman da Abbas Sani Abbas na ma’aikatar raya karkara.

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati, da kuma taimaka wa gwamnan wajen kai romon dimokuraɗiyya ga ƴan jihar.

Haka kuma gwamnan ya yi wa wasu kwamishinonin sauyin ma’aikatu, waɗanda suka haɗa da: “mataimakin gwamnan jihar, wanda aka sauya masa ma’aikata daga ƙananan hukumomi zuwa ma’aikatar ilimi mai zurfi, da Mohammad Tajo Usman daga ma’aikatar kimiyya da fasaha zuwa ma’aikatar ƙananan hukumomi, da Dr Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata daga m’aikatar ilimi mai zurfi zuwa kimiyya da fasaha.”

Sauran sun haɗa: “Hajiya Amina Abdullahi daga ma’aikatar jinƙai da rage talauci zuwa ma’aikatar mata, da Nasiru Sule Garo daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman da Haruna Doguwa daga ma’aikatar ilimi zuwa ma’aikatar albarkatun ruwa.”

Sai dai gwamnan ya buƙaci waɗanda aka cire ɗin su je ofishin gwamna domin a ba su wani aikin daban.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp