Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin sarakuna uku masu daraji ta biyu a jihar.
Sanarwar da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature ya fitar ta ce sarakunan da aka amince a naɗan sun haɗa da Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin sarkin Karaye da Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin sarkin Rano da kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sarkin Gaya.
Sanarwar ta ce naɗin sabbin sarakunan zai ya fara aiki nan take.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya sanya hannu a kan ƙudirin dokar masarautar Kano ta 2024, wadda majalisar dokokin jihar ta yi wa gyaran fuska.
Gwamnatin jihat ta ce an yi wa dokar kwaskwarima ne dominn farfaɗo da haƙiƙanin al’adun jama’ar jihar.
A bisa sabon tsarin di, masarautar Rano ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da kuma Bunkure.
Sai masarautar Gaya da ta ƙunshin ƙananan hukumomin Gaya da Albasu da kuma Ajingi. Da kuma masarautar Ƙaraye da ta ƙunshi Ƙaraye da kuma Rogo.
Gwamna Abba Ƙabir ya yi bayanin cewa sabbin sarakunan masu daraja ta biyu za su tallafawa Sarkin Kano mai daraja ta ɗaya wajen tafiyar da harkokin mulki a masarautun nasu.