Gwamna jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da martani a karon farko, bayan shafe watanni ana rade-radin tsige sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi.
Gwamnan, wanda ya yi magana a lokacin da yake rantsar da sabbin sakatarorin dindindin da masu ba shi shawara na musamman a zauren majalisar dokokin jiha a ranar Talata, ya ce babu wata farfaganda da za ta hana gwamnatinsa cimma burinta.
Ya ce, wasu na ta jita-jita cewa sun samu sabani da sakataren gwamnati, kuma wannan zancen shaci fadi kawai.
Kuma koyaushe suna ƙoƙarin haifar da jita-jita don haifar da tashin hankali a gwamnatinsa.
Gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu Abdullahi Baffa Bichi, yana samun sauki daga rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma da zarar ya dawo zai karbi ragamar aikinsa inda ya tsaya.


