Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananna hukumomin jihar da ke guda.
Abba Kabir ya kaɗa ƙuri’ar ne a rumfar zaɓensa ta Chiranci a mazaɓar Diso ta ƙaramar hukumar Gwale.
Yayin da yake jawabi bayan kaɗa ƙuri’ar, gwamnan ya ce zaɓn na gudana cikin kwanciyar hankali.
Jam’iyyar APC mai hamayya a jihar dai ba ta shiga zaɓen ba.