fidelitybank

Gwamnan Kaduna ya rage kuɗin makarantun jihar saboda tsadar rayuwa

Date:

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya amince da rage kuɗin makaranta a manyan makarantu na jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin rage irin wahalhalun da tsadar kuɗin makaranta ke haifarwa ga al’ummar jihar.

Sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari na kuɗin makaranta da ɗalibai ke biya a jami’ar jihar Kaduna, wato KASU.

Haka nan an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari na kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria.

Bugu da ƙari sanarwar ta ce an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a Kwalejin ilimi ta jihar da ke Gidan Waya.

Yayin da aka yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai masu karatun babban difiloma ke biya a Kwalejin koyar da harkokin lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi, inda su ma masu karatun difiloma za su samu ragin kashi talatin cikin ɗari.

A ƙarshe sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin koyon jinya ta jihar

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp