Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya amince da Naira miliyan 1 a matsayin tallafi ga kowane mahajjatan jihar da za su yi aikin Hajjin shekarar 2024.
Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
Hakan ya biyo bayan karin farashin kudin da hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi a baya bayan nan, sakamakon yadda farashin canji ya samu karbuwa.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Kabiru Gombe, ya bukaci gwamnatin Najeriya da gwamnonin jihohin kasar da su kai dauki ga maniyyata.
Labbo ya bukaci maniyyatan jihar da su tabbatar sun mika sauran kudaden da suka rage na sama da N918,000 ga hukumar.
Ya yi nuni da cewa wadanda za su ci gajiyar tallafin aikin Hajji su ne wadanda tuni suka biya wani bangare na kudaden da hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta yi.
Hukumar NAHCON ta sanar da karin kudin aikin Hajji da N1,918,032.91, wanda ya kai adadin zuwa N6,617,032.91.