Gwamnatin jihar Jigawa, ta raba tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda gobarar tankar man fetur ta rutsa da su.
Ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama’a ne suka bayar da tallafin tun lokacin da gobarar ta tashi a bara, inda aka samu fiye da naira miliyan dubu daya.
Sai dai gwamnatin ta ce ba duka bane suka zo hannu.
Zuwa yanzu an raba wa mutum 210 naira miliyan 840.
An bai wa kowanne naira dubu ɗari biyar a hannu, inda daga bisani za a saka sauran miliyan 3 da rabi a asusun ajiyarsu ta banki.
A watan Oktoban bara ne wata motar dakon mai ta kife a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura da ke jihar Jigawa, bayan ta taso daga jihar Kano a kan hanyarta ta zuwa jihar Yobe.
Daga bisani motar ta kama da wuta wanda ya yi sanadiyar kashe mutane fiye da 200 da ake tunanin suna ƙoƙarin ɗibar fetur ɗin da ke zuba a motar da ta faɗi ne.