fidelitybank

Gwamnan Jigawa ya dakatar da Kwamishinan da aka kama a Kano da zargin lalata da Matar aure

Date:

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya dakatar da kwamishinan ayyuka na musamman, Auwalu Danladi Sankara bisa zargin da hukumar Hisba ta jihar Kano ta yi masa na ”lalata da wata matar aure”.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ya ce an ɗauki matakin ne domin samun damar gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa kwamishinan.

Ya ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiya da kuma kare martabar gwamnatin jihar.

A ranar juma’a ne dai hukumar Hisba ta jihar Kano ta fitar da sanarwar kama kwamishinan bisa zarginsa da mu’amala da matar aure a wani gida da ba a kammala ba, a jihar Kano.

“Muna ɗaukar duka zarge-zargen da muhimmanci kuma za mu yi bincike da nufin fito da gaskiya domin duka ƴan jihar Jigawa su gani,” in ji sakataren gwamnatin jihar.

Ya kuma ce an ɗauki matakin dakatar da kwamishinan ne domin yin sahihin bincike da kuma yin adalci ga kowane ɓangare.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce abin kunya ne abin da ake zargin kwamishinan da aikatawa kuma cin fuska gare ta.

Tuni kuma gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti mai mambobi huɗu waɗanda za su yi bincike da kuma gabatar da rahoto cikin mako biyu kacal.

daily post nigeria today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp