Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya yi alhinin rasuwar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Nasiru Nono, wanda ya rasu ranar Alhamis a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Abuja zuwa Keffi.
A cikin wata sanarwa daga Ismaila Uba-Misilli, Darakta-Janar, hulda da manema labarai na gidan gwamnatin Gombe, Yahaya ya bayyana alhininsa game da mutuwar Nono.
Yahaya ya bayyana rasuwar Nono a matsayin babban rashi ga iyalansa, Gombe da Najeriya baki daya.
Karanta Wannan:Â Na ci zabe na ba tare da Peter Obi ba – Zababben gwamnan Abia
Ya ce marigayi tsohon dan majalisar ya gudanar da aikinsa na majalisar ne da “hankali, tsantseni da sanin yakamata a lokacin da yake shugabancin majalisar dokokin jihar kuma ya samu karramawa da biyayya daga abokan aikinsa.
Sai dai ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya jikan marigayiyar Aljannar Firdausi.