Gwamnatin jihar Filato ta zargi jami’an sojojin ƙasar da sakaci wajen rashin kama maharan da suka kashe mutum 27 a garin Tahoss na yankin ƙaramar hukumar Riyom.
A farkon makon nan ne wasu mahara ɗauke da makamai suka auka wa garin tare da halaka mutum 27 da raunata wasu.
Yayin wata hira da gidan talbijin na Channels ranar Juma’a ta cikin shirin ”The Morning Brief” kwamishiniyar yaɗa labaran jihar, Joyce Ramnap ta ce sojojin da ke yankin sun nuna sakaci wajen rashin kama ko da mutum guda cikin maharan, duk kuwa da kasancewar sojojin a kusa da garin.
Kwamishiniyar ta ce garin da aka kai harin na kusa da shingen binciken ababen hawa da sojoji ke gudanarwa.
“Akwai shingen binciken ababen hawa na sojoji, wanda bai fi tazarar mita 200 daga wurin da lamarin ya faru, kuma daga bayanan da muka samu ba wanda suka kama, kuma ba su kashe kowa ba”.
“Garin nan ba wani gari ba ne mai nisa da za a ce kafin a kai inda suke an yi musu lahani, suna kusa da titi,” in ji ta.