Gwamnan Jihar Ekiti a kudancin Najeriya, Kayode Fayemi, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki ta APC a babban zaɓe na 2023.
Fayemi wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnoni ta Najeriya, ya ce zai tabbatar da “kyakkyawan shugabanci da haɗin kan ƙasa” idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Gwamnan zai kara da sauran ‘yan takara a APC da suka haɗa da Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo waɗanda suka fito daga shiyya ɗaya ta Kudu maso Yamma. Kazalika akwai Gwamnan Kogi Yahaya Bello, da Gwamnan Ebonyi David Umahi, da sauransu.
APC ta sanya ranar 30 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yuni, don gudanar da zaɓukan fidda gwani tsakanin ‘yan takarar.